Gaba daya dai rundunar sojojin ruwan kasar Sin ta shafi shekaru hudu tana aikin gina wannan sabuwar tasha mai saukar babbar jirgin ruwa, wadda ke kunshe da dukkan kayayyakin aiki, ciki hadda ruwa, da wutar lantarki, da iskar gas, da man fetur da dai sauransu. Kuma wannan babban jirgin ruwa na LiaoNing, zai ci gaba da aikin gwaji da na horaswa a tashar.
A ranar 26 ga wata ne dai jirgin na Liaoning, ya tashi daga tashar jirgin ruwa ta kamfanin kirar jiragen ruwa na Dalian, kuma yayin da yake tafe, an yi gwajin naurorin soja a kansa, bisa shirin da aka tsara. (Maryam)