Yanzu dai Lyon din ce ke saman Marseille dake a matsayi na biyu.
Dan wasan Lyon Alexandre Lacazette ne dai ya jefa kwallaye 2 a ragar abokan karawar su, wanda hakan ya sanya jimillar kwallayen da ya ci kaiwa 19 a kakar wasannin bana, kafin kuma Nabil Fekir ya jefa kwallo ta 3 a ragar Toulouse bayan dawowa hutun rabin lokaci.
Da wannan sakamako kulaf din na Lyon ya samu cimma nasarar lashe kofin kasar ajin kwararrun kasar har karo 7, tare da dara Marseille da maki daya, sakamakon rashin nasarar da Marseille din ta samu a hannun Montpellier da ci 2 da 1 a wasan su a ranar Juma'ar da ta gabata.
Sauran kulaflikan da ke kan gaba a teburin dai sun hada da St Etienne a matsayi na 3, sai kuma Paris Saint Germain dake matsayi na 4.
Can a kasan teburin kuwa, maki daya ya ragewa kulaf din Toulouse ya fada relegation, ya yin da a can kasa Evian Thonon Gaillard ke matsayi na 18, sai Lens a matsayi na 19, ya yin da kuma Caen ke matsayi na 20.(Saminu Alhassan Usman)