in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na fatan sassa daban daban na Yemen za su aiwatar da shirin shimfida wani tsarin siyasa na wucin gadi ta hanyar tattaunawa
2014-09-22 20:10:59 cri
Dangane da daddale yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a tsakanin gwamnatin kasar Yemen da kungiyar Houthi a daren ranar Lahadi 21 ga wata, wadda ta kawo karshen rikicin zubar jini da aka samu a birnin Sanaa har na tsawon mako daya, madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana yau Litinin 22 ga wata cewa, kasar Sin na fatan sassa daban daban na Yemen za su kawar da sabanin da ke tsakaninsu ta hanyar yin tattaunawa da shawarwari, za su kuma ci gaba da kokarin aiwatar da shirin shimfida wani tsarin siyasa na wucin gadi, a kokarin maido da kwanciyar hankali da bunkasuwa a kasar ta Yemen cikin hanzari. (Tasallah)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China