in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An zartas da sanarwar tabbatar da tsaron makamashin nukiliya ta Vienna
2015-02-11 10:52:28 cri
Kasashe masu ruwa da tsaki game da yarjejeniyar tsaron makamashin nukiliya sun zartar da sanarwar tabbatar da tsaron makamashin ta Vienna, ya yin taron da suka gudanar a ranar Litinin, a helkwatar hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA dake birnin Vienna.

Sanarwar wadda ta kasance mai muhimmanci ga taron, ta kasance mai matukar ma'ana a tarihin yarjejeniyar tsaron makamashin nukiliya. Kaza lika ta kunshi yabo ga kasashen da suka daddale yarjejeniyar, bisa matakin da suka dauka na kyautata aikin tabbatar da tsaron makamashin nukiliya, bayan aukuwar hadarin Fukushima na kasar Japan.

Har wa yau sanarwar ta bukaci da a kara gudanar hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya, wajen inganta karfin tabbatar da tsaron nukiliya, da bukatar kasashen dake cikin yarjejeniyar, wadanda kuma suka kafa sabbin tasoshin samar da wutar lantarki na nukiliya, su kiyaye ka'idojin tabbatar da tsaron makamashin, baya ga bukatar da aka bayyana ta bangarori daban daban su aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata.

Ya yin taron shugaban tawagar kasar Sin Liu Hua, ya bayyana manufar kasar Sin, game da tabbatar da tsaron makamashin nukiliyar ta, da ma na sauran sassan duniya baki daya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China