in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashe 5 dake da makaman nukiliya sun tsaida kudurin hana sarrafa nukiliya
2015-02-06 16:03:26 cri
Kasashe 5 dake da makaman nukiliya wato Sin, da Amurka, da Rasha, da Britaniya da kuma Faransa, sun kira taro na aiwatar da yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya.

Ya yin taron wanda ya gudana daga ranar 4 zuwa 5 ga watan nan, wakilan kasashen sun zanta game da kudurorin tabbatar da tsaron kasa da kasa, da yadda ake aiwatar da yarjejeniyar dakile yaduwar makaman nukiliya, da tabbatar da amfani da makamashin nukiliya cikin lumana. Sauran ababen da aka tattauna sun hada da batun hadin gwiwa tsakanin kasashen biyar kafin kuma su fidda hadaddiyar sanarwar bayan taron.

Game da hakan, kasar Sin ta bayyana cewa kamata ya yi, kasashen biyar su kara fadada mu'amala, da daidaita ra'ayoyinsu, da bayyana kansu a matsayin masu himmar aiwatar da yarjejeniyar hana yaduwar makaman na nukiliya, su kuma jagoranci aikin rage makaman nukiliyar.

Kaza lika Sin na fatan kasashen zasu dage wajen hana yaduwar makaman nukiliya, su kuma tabbata cewa ana amfani da makamashin nukiliya ta hanyoyin lumana kadai, tare da ganin ana sarrafa harkokin nukiliya na duniya bida doka, da tabbatar da aiwatar da kudurorin tsaron kasa da kasa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China