Kungiyar tarayyar Afirka ta AU ta shirya wani taro na yini biyu, domin tattauna muhimman batutuwan da suka jibanci tsara ci gaban nahiyar Afirka.
Taron wanda shi ne irinsa na 14, da aka bude a ranar Alhamis a birnin Adis Ababa na kasar Habasha, mai taken "tallafin MDD ga shirin kungiyar AU nan da shekarar 2063", ya samu halartar wakilai daga hukumomin MDD, da shuwagabannin kungiyar ta AU.
Ana kuma fatan wannan taro zai baiwa hukumomin dake karkashin MDDr damar samar da tallafin hanyoyin da za a bi, domin tabbatar da nasarar tsare-tsaren da AU ke aiwatarwa domin ci gaban nahiyar Afirka nan da shekaru 50 masu zuwa.
Da yake jawabi yayin bikin bude taron, babban magatakardar hukumar bunkasa tattalin arzikin Afirka ta MDD UNECA, Mr. Carlos Lopes, cewa ya yi, taron na wannan lokaci, zai samar da hanyoyin daidaita shirye-shiryen yankuna da na shiyya-shiyya da ake aiwatarwa domin ci gaban nahiyar. Ya ce, abun lura shi ne, nauyin bunkasa nahiyar ta Afirka na wuyan al'ummarta, yayin da aikin MDD a wannan sashe bai wuce ba da tallafi ba.
Shi ma a nasa jawabi, mataimakin hukumar zartaswar kungiyar ta AU Erastus Mwencha, ya ce, batutuwan da suka shafi bunkasa zaman lafiya, da tsaron rayukan al'umma, da samar da ababen more rayuwa, na cikin muhimman ababen da AU ke hadin gwiwa da MDD wajen ganin wanzuwar su.
Ana sa ran tattaunawa ta gaba kan sakamakon wannan taro cikin watan Janairun shekarar 2014 dake tafe, kafin a kai ga amincewa da sakamakon cikin watan Mayun shekarar ta badi. (Saminu)