in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asusun taimakawa bunkasuwar Afirka na kasar Sin ya taka rawa mai kyau
2013-10-18 18:12:49 cri


Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nuna a yayin ziyararsa a nahiyar Afrika a watan Maris na wannan shekara cewa, "Sin na dukufa kan hade bunkasuwarta da na Afrika, har ma hade da moriyar Sinawa da na 'yan Afrika, sannan kuma da hade zarafin samun bunkasuwarta da na Afrika." A halin yanzu, asusu kadai da Sin ta kafa wajen goyon bayan kamfanonin kasar Sin da suka zuba jari a Afrika wato asusun taimakawa bunkasuwar Afrika na kasar Sin yana gudanar da aikinsa yadda ya kamata a Nahiyar.

An kafa wannan asusu ne a watan Yuni na shekarar 2007, wanda ya kasance daya daga cikin manyan matakai 8 da gwamnatin Sin ta sanar za ta dauka a gun taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin kai tsakanin Sin da Afrika da aka yi a shekarar 2006. Ya zuwa yanzu, bankin raya kasar Sin ta samar da kudin dala biliyan 3 domin gudanar da aiki na mataki na daya da biyu na asusun, kudin da ake yin amfani da su wajen taimakawa wasu kamfanonin kasar Sin wadanda suka zuba jari a nahiyar Afrika, tare kuma da samar musu hidima ta fuskar bayanai.

Mai kula da harkokin reshen asusun a kasar Ghana Chu Shuntang ya ce, ana yin kokarin taimakawa wasu ayyuka wadanda za su biya bukatun al'ummar Afirka da kawo moriyar bangarorin biyu musamman ma wadanda za su ba da taimako wajen raya Afrika, ciki hadda sha'anin karfe, sha'anin noma, masana'antar samar da wutar lantarki, kamfanin jiragen sama, yankin cikini cikin 'yanci, da yawon shakawata da dai sauransu.

Bisa labarin da aka bayar an ce, masana'antar samar da wutar lantarkin nan mai suna Kpone da ke karkashin kamfanin Sunon Asogli Power(Ghana) da kamfanin samar da makamashi na Shenzhen na kasar Sin da asusun bunkasa Sin da Afirka suka zuba jari , ta kasance ta farko da kamfanin kasar Sin ya zuba jari kai tsaye a Afrika, har wa yau, tana taka muhimmiyar rawa a wajen samar da wutar lantarki a kasar Ghana, wadda take samar da wutar lantarki na kashi 12 zuwa 14 cikin dari bisa na dukkan wutar lantarki da kasar ta kan samar a cikin shekara. Ban da haka, kamfanin zirga-zirgan sama AWA a kasar Ghana wanda asusun da kamfanin zirga-zirgan sama na lardin Hainan na kasar Sin suka zuba jari wajen kafa shi, ya cimma nasara wajen baiwa hidima ga shugabar kasar Liberia a yayin ziyararta a kasar Ghana da ta Saliyo.

Game da batun dalilin da ya sa aka zuba jari ga sha'anin zirga-zirgan sama, wakilin asusun da ke kasar Ghana kuma mai sa ido kan harkar kudi na AWA He Yali ya ce, ba ma kawai ana bukatar manyan ababen more rayuwa da sha'anin kere-kere ba saboda ganin bunkasuwar nahiyar Afirka, har ma ana bukatar bunkasuwar harkokin zirga-zirga. Sakamakon yadda ake fuskantar koma bayan harkokin zirga-zirgar mota da na jiragen kasa, ya sa ake matukar bukatar raya sha'anin zirga-zirgan sama. Hakan ya sa asusun da kamfanin zirga-zirgan sama na lardin Hainan sun yi hadin kai sun zuba jari domin kafa kamfanin AWA, wanda ya fara gudanar da harkokin zirga-zirga a watan Satumba na shekarar 2012. A yanzu haka, kamfanin na gudanar da harkokinsa ta hanyoyi uku a cikin gida, wanda harkokin da yake gudanar ya kai kashi 15 bisa 100 na gaba dayan harkokin zirga-zirgar jiragen sama na kasar ta Ghana.. A watan Nuwamba na bana, kamfanin zai kaddamar da hanyar zirga-zirga zuwa ga kasar Nijeriya da Saliyo, sa'an nan a shekara mai zuwa, zai fara harkokin zirga-zirga zuwa ga Libiya, Senegal da Gambia.

Ban da kafa reshensa a Ghana, asusun ya kafa sassansa a kudanci, gabashi da tsakiyar Afrika, har ma yana shirin kafa wata hukuma mai kula da harkokin kungiyar tarayyar kasashen gabashin Afrika ta EAC a birnin Nairobi babban birnin kasar Kenya, domin ba da taimako a fannin zuba jari ga mambobin kasashen kungiyar, ciki hadda Kenya, Tazaniya, Uganda, Ruwanda da Burundi, har ma da Sudan ta kudu za ta shiga kungiyar ba da jimawa ba. Wakilin reshen asusun a gabashin Afrika Liu Jie ya nuna cewa, ya zuwa yanzu, asusun ya zuba jari ga shirye-shirye uku a kungiyar EAC, ciki hadda shirin sama da shirye-shiryen talibiji ta yi amfani da fasahar zamani, da sha'anin hakar kwal da karfe da sauransu wadanda suka shafi kudi dala miliyan 105. Manyan fannoni uku da aka fi mai da hankali wajen zuba jari a gabashin Afirka sun hada da samar da makamashi, gina gidaje, da kuma sha'anin kere-kere, an yi kiyasin cewa, za a zuba makudan kudaden jari a kasashen EAC.

A ganin Mr. Liu Jie, Sin ta canja hanyarta a fannin shigi da fice, wato ta fara zama kasar da take fitar da jari da fasaha zuwa kasashen waje a maimakon kasar da take shigowa da kaya daga ketare. Bisa tsarin da kasar ta yi, Kenya da sauran kasashen kungiyar EAC za su zama yankin da ya fi samun bunkasuwar tattalin arziki a Afrika, abin da ya sa za su kara bukatar jari daga kasashen waje, a hannu daya kuwa, suna kara jawo hankalin masu zuba jari a duniya, saboda haka, wasu kamfanonin kasa da kasa sun kaurar da cibiyoyinsu zuwa Kenya. Hakan ya sa, kamar yadda dangantakar kut da kut tsakanin Sin da EAC a fannin siyasa suke bunkasa, dangantakar dake tsakaninsu ta fuskar zuba jari, kawo moriyar juna da yin hadin kai za ta bunkasa yadda ya kamata.

An ba da labari cewa, asusun ya zama wani muhimmin jigo wajen ba da jagoranci ga kamfanonin kasar Sin wajen zuba jari a Afirka bayan kokarin da ya yi cikin shekaru 6 da suka gabata, wasu ayyuka da suka yi a Afirka sun zama abubuwan shaida ga ci gaban da aka samu a fannin hadin gwiwar Sin da Afrika, hakan ya sa ya samu yabo daga shugabanni da jama'ar kasashen Afirka da dama. Har zuwa yanzu, yawan kudin da asusun ya zuba wa Afrika ya kai dala biliyan 1.9, ban da haka, ana sa ran asusun zai kaddamar da aikinsa na mataki uku da zai shafi kudi dala biliyan 2 a shekarar 2014. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China