Yayin da yake yi bayani kan sakamakon da aka samu daga hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, Zhang Ming ya bayyana cewa, yawan kudin da aka samu a harkokin ciniki a tsakanin Sin da Afirka ya karu cikin sauri, inda a shekarar 2013 ya kai dala biliyan 210, wanda ya ninka sau 21 bisa na shekarar 2000. Kana an samu saurin bunkasuwar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a fannonin zuba jari da tattara kudi, sannan an gudanar da ayyukan hadin gwiwa a tsakaninsu a fadin nahiyar Afirka. An kuma yi mu'amala sosai a tsakanin jama'ar Sin da Afirka, yawan Sinawa da suka ziyarci kasashen Afirka a shekarar 2013 ya kai miliyan 1 da dubu 895, kana yawan 'yan kasashen Afirka da suka zo kasar Sin ziyara a shekarar ya kai dubu 553.
Hakazalika kuma, Zhang Ming ya jaddada cewa, shekarar badi shekara ce da cika shekaru 15 da kafa dandalin tattaunawa a tsakanin Sin da Afirka, kasar Sin tana fatan ita da bangaren Afirka za su gudanar da taron ministoci karo na 6 na dandalin tattaunawar yadda ya kamata, da kara inganta sabuwar dangantakar abokantaka a tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi. (Zainab)