An gudanr da bikin nune-nunen al'adun hanyar Siliki ta ruwa da ta hada Sin da kasashen Afirka a kasar Tanzania
A kwanakin baya, hukumar kula da kayayyakin tarihi ta kasar Sin, da ma'aikatar lura da albarkatun halittu da yawon shakatawa ta kasar Tanzania, da ofishin jakadancin Sin dake kasar Tanzania sun shirya wani biki na nune-nunen al'adun hanyar Siliki ta ruwa, wadda ta hada Sin da kasashen Afirka, a wani mataki na murnar cika shekaru 50 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Tanzania.
An ce an gudanar da wannan biki ne a dakin adana kayayyakin tarihi na kasar Tanzania, a wani bangare na bikin wata guda da kasar ta gudanar, inda aka nuna kayayyaki 41 daga bangaren Sin, da kuma kayayyakin tarihi na kasar Sin 24 da kasar Tanzania take da su.
Wannan ne kuma karon farko da aka fidda wadannan kayayyakin tarihi na Sin da dakin adana kayayyakin tarihi na kasar Tanzania ya mallaka a bainal jama'a. (Zainab)