in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsarin PPP ba ma'uni daya kacal ba ne wajen kwatanta karfin tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka
2014-10-10 15:01:18 cri

Shugabar asusun ba da lamuni na duniya (IMF) Christine Lagarde ta yi bayani a ranar Alhamis 9 ga watan nan da muke cik cewa, ko da yake a bana kasar Sin za ta wuce kasar Amurka wajen zama kasa ta farko da ke samun saurin bunkasuwar tattalin arziki a duniya bisa alkalumann farashin kayayyaki wato PPP, ko da yake ya kamata a yi la'akari da jerin batutuwa wajen kimanta karfin tattalin arzikin kasa.

Bisa sabuwar kididdigar da IMF ta fitar, an nuna cewa, idan aka yi kididdiga bisa tsarin alkaluman PPP, to yawan kudin da kasar Amurka ta samu daga sarrafa dukiyar kasa ya kai dalar Amurka biliyan 17400 a shekarar 2014, a nata bangaren ma yawan kudin da kasar Sin ta samu ya kai dala biliyan 17600.

A gun taron manema labaru da aka shirya a yayin taron shekara-shekara na asusun IMF da Bankin duniya, madam Lagarde ta bayyana cewa, yawan kason da kasar Sin ta samu a fannin tattalin arziki na samun karuwa bisa tsarin alkaluman PPP, amma duk da haka, tana baya bisa ma'aunin GDP.

Lagarde ta kara da cewa, kamata ya yi kasar Amurka ta amince da shirin yin kwaskwarima kan batutuwan da suka shafi kason kasashe mambobi da tsarin gudanarwa na asusun IMF na shekarar 2010, ta kuma fahimci muhimmancin ayyukan yin kwaskwarima na karfafa matsayin wakilci da IMF zai samu kan harkokin tattalin arzikin duniya, wato kara ba da ikon bayyana ra'ayi ga kasashe masu saurin bunkasuwa ciki har da kasar Sin. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China