Kasashen Algeria da Ghana sun cimma nasarar kaiwa wasan kusa da na kusan karshe, a ci gaba da buga gasar cin kofin Afirka AFCON ta bana dake gudana a Equatorial Guinea.
A wasannin rukunin C da suka buga jiya Talata, kasar Algeria wadda a baya bayan nan hukumar FIFA ta bayyana a matsayin mafi kwarewa a fagen buga tamaula a nahiyar Afirka, ta samu nasarar doke Senegal da ci 2 da nema.
A daya wasan da ya gudana a filin wasa na Mongomo kuwa, Ghana ce ta samu nasara kan Afirka ta Kudu da ci 2 da 1.
A Larabar nan kuma, akwai wasa tsakanin Guinea da Mali, da kuma wasan Kamaru da Cote d'Ivoire, wasannin da za su fidda zakarun rukunin na D.
A wasannin kusa da na kusan karshe da ke tafe ran 31 ga watan nan, kasar Congo za ta taka leda da janhuriyar dimokaradiyyar Congo, yayin da kuma Tunisia za ta kece raini da mai masaukin baki wato Equatorial Guinea.
A ranar 1 ga watan Fabarairu kuwa, Algeria za ta fafata da kungiyar da za ta kasance ta daya a rukunin D, yayin da ita kuma Ghana za ta buga nata wasa a wannan rana da kungiya ta daya a rukunin na D. (Saminu)