in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gasar AFCON rukunin B
2015-01-27 10:25:36 cri

A ci gaba da buga gasar cin kofin Afirka dake gudana yanzu haka a kasar Equatorial Guinea, a jiya Litinin Cape Verde ta tashi wasanta da Zambia kunnen doki maras ci.

Kana ita ma Tunisia ta tashi canjaras 1 da 1, da Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo.

Yanzu haka dai Tunisia ce ke saman teburin rukunin na B da maki 5, sai Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo da Cape Verde dake biye da maki uku-uku. Sai kuma Zambia dake matsayi na karshe da maki 2. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China