Kamfanin hanyoyin jiragen kasa na kasar Sin (CRCC), ya kammala aiki aikin ginawa da zamanintar da hanyoyin layin dogo tsakanin Abuja, babban birnin kasar, da jihar Kaduna dake arewa maso yammacin kasar Najeriya.
Ministan sufurin Najeriya, Idris Umar, ya daure kusar karshe ta hanyar layin dogon a yayin bikin kammala aikin, dake tabbatar da kammala matakin farko na aikin layin dogo na wannan kamfani dake aiki a Najeriya da kuma yammacin Afrika, in ji kamfanin CRCC. Shekaru uku aka kwashe ana aikin wanda ya shafe kusan dalar Amurka miliyan 850, haka kuma layin dogon na da tsawon kilomita 1865, tare da saurin gudu na kilomita 150 a cikin awa guda. (Maman Ada)