Shugaban Nigeriya Goodluck Jonathan a ranar Talatan nan ya ce, gwamnatinsa ta inganta kokarin da take yi na mai da layukan dogon kasar na zamani don ci gaban kasar da bunkasarta.
Shugaban wanda ya fadi hakan a lokacin kaddamar da jirgin kasa na fasinja mai amfani da man diesel wato DMU tsakanin Abuja zuwa Kaduna mai tazaran kilomita 220 arewacin Abujan, babban birnin tarayyar kasar, ya ce, gyara tare da mai da layin dogon na zamani zai kawo ci gaban kasa da bunkasarta.
Ya ce, a cikin shekaru 30 da suka gabata, bangaren sufurin jiragen kasa sun fuskanci rashin kula matuka, don haka gwamnatin za ta cika burin al'ummar kasar na ganin an farfado da wannan bangare yadda ya kamata, kuma ya ci gaba da zama a kan gaba cikin ayyukan da gwamnati za ta mai da hankali a kai.
Tun da farko shugaban hukumar jiragen kasa ta Nigeria Adeseyi Sijuade ya ce, jiragen kasa na zirga zirga na cikin gari zai yi aiki ne kafada da kafada tsakanin hukumar da gwamnatin jihar Kaduna domin inganta sufuri a jihar.
Adeseyi Sijuade ya ce, wani jirgin mai saurin gaske sosai da zai yi zarya tsakanin Abuja da Kaduna za'a kaddamar da shi a farkon watannin uku na shekarar 2015, a cewar shi, wannan jirgi zai rika tafiya a kilomita 180 a cikin awa daya wanda zai taimaka matuka ga ma'aikatan dake zaune a Kaduna suke aiki a Abuja.
Shi dai jirgin na DMU, a cewar Sijuade, zai yi tafiya ne a kilomita 100 a cikin awa daya, kuma zai dauki fasinja 540 a lokaci daya. (Fatimah)