in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Amurka ya yi gaban kansa wajen ganawa da Dalai Lama
2014-02-22 17:05:00 cri
Shugaba Barack Obama na Amurka, ya gana da Dalai Lama a fadar sa ta White House a jiya Jumma'a 21 ga wata, ba tare da la'akari da rashin amincewar da kasar Sin ta nuna don gane da hakan ba.

Wannan ne dai karo na uku, da Obama ya gana da Dalai Lama a matsayin sa na shugaban Amurka. Matakin da ya sanya kasar Sin yin suka da kakkausar murya.

Mataimakin ministan harkokin wajen Sin Zhang Yesui, ya kira mukaddashin jakadan Amurka a kasar Sin domin ganawa da shi nan take, inda ya bayyana rashin amincewar kasar ta Sin.

Zhang ya ce, wannan danyan aiki da Amurka ta yi, tamkar tsoma hannu cikin harkokin cikin gidan kasar Sin ne, kuma ya saba wa alkawarin da Amurkan ta yi na cewa, ba za ta goyi bayan yunkurin samun 'yancin kan Tibet ba. Har wa yau matakin ya keta ka'idojin dangantakar kasashen duniya, ya kuma haifar da babbar illa ga dangantakar Sin da Amurka.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar ta Sin ya kara da cewa, tuni Amurka ta amince da ikon Sin na mallakar jihar Tibet, kuma ta ce ba za ta goyi bayan yunkurin samun 'yancin kan Tibet ba. A hannu guda kuma ta shirya ganawa da Dalai Lama, wanda ke matsayin madugun kungiyar masu yunkurin kawowa kasar Sin baraka. Hakika wannan danyen aiki na Amurka, zai yi babbar illa ga hadin gwiwa, da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma moriyar kasar Amurka.

Sin ta kalubalanci Amurka da ta yi la'akari da matsayin da gwamnatin Sin dauka dangane da batun, domin cika nata alkawari, na amincewa da ikon Sin na mallakar jihar Tibet, ta kuma dauki matakai nan take na kawar da mummunan tasiri da ake gudu. Haka kuma Sin na bukatar Amurka ta daina tsoma baki cikin harkokin gidan ta, ta hanyar amfani da batun jihar Tibet, tare da kauracewa goyon bayan ta ga mummunar manufar kungiyar Dalai ta kawowa kasar Sin baraka.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China