Mai kula da kwamitin harkokin waje na NPC ya yi bayani kan ganawa tsakanin 'yan majalisar dokokin Amurka da Dalai
Yau Jumma'a 7 ga wata, mai kula da kwamitin harkokin waje na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin(NPC) ya yi bayani kan ganawa tsakanin 'yan majalisar dokokin kasar Amurka da Dalai Lama cewa, jiya 6 ga wata, shugaba da wasu membobin majalisar dokokin kasar Amurka sun kyale kiyayyar gwamnatin kasar Sin sun gana da Dalai Lama, hakan ya keta alkawarin Amurka na ba za ta nuna goyon baya ga 'yan a-ware na jihar Tibet ba, kuma ya sa hannu cikin harkokin gida na Sin. Majalisar NPC ta nuna rashin amincewa da hakan da babbar murya.(Fatima)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku