Kakakin ta yi nuni da cewa, harkar da ta shafi Tibet harkar cikin gida ce ta kasar Sin, wadda bai kamata ba wata kasar waje ta tsoma baki a ciki. Dalai Lama ya dade yana yunkurin neman jawo baraka ga kasar Sin inda yake fake da addini. Don haka, ganawar da shugaban kasar Amurka zai yi da Dalai Lama tamkar tsoma baki ne a cikin harkokin gida na kasar Sin, wadda za ta keta ka'idar da ta shafi huldar da ke tsakanin kasa da kasa, wadda kuma za ta iya lalata huldar da ke tsakanin Sin da Amurka. Don haka, kasar Sin na nuna matukar rashin amincewarta.(Lubabatu)