Tawagar MDD ta yi kashedi kan illolin wannan matsala ga muhalli da kuma tattalin arziki bayan wannan tashin hankali da kuma lalata gine-gine a wannan yankin da ake kira na "ci gaban man fetur", tare da yin kira ga dakarun dake fagen daga da su bada hadin kai domin baiwa 'yan kwana-kwana damar kashe gobarar.
Haka kuma tawagar da a tsagaita bude wuta, har ma da na hare-haren jiragen yaki, dake barazanar bazuwar yakin cikin wannan kasa.
Wadannan hare-haren suna take kudurorin kwamitin sulhu na MDD a kasar Libiya. Man fetur na Libiya na al'ummar kasar Libiya gaba daya kuma shi ne ginshikin tattalin arzikin kasar, in ji MANUL.
Haka kuma tawagar MDD ta yi allawadai da harin ranar Alhamis da wasu mutanen da ba a tantance ba suka kai, da janyo asarar rayuwakan masu gadin tashar wutar lantarki dake kusa da birnin Syrte. (Maman Ada)