in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tunisia ta doke Zambia a ci gaba da gasar AFCON
2015-01-23 10:27:41 cri

Tunisia ta samu nasarar doke Zambia da ci 2 da 1, yayin wasan rukunin B da kasashen biyu suka buga a jiya Alhamis. Wannan sakamakon dai ya baiwa Tunisian damar darewa matsayin farko a teburin rukunin na biyu da maki 4.

Yan wasan Tunisia Yasine Chikhaoui, da Ahmed Akaichi ne dai suka zura kwallayen biyu a ragar Zambia, yayin da 'dan wasan Zambia Emmanuel Mayuka, ya zura kwallo daya tilo ga kasarsa.

A daya wasan da aka buga a jiyan kuwa, jamhuriyar dimokaradiyyar Congo ta tashi wasan ta Cape Verde babu ci.

A wasanta na gaba, Tunisia za ta kara ne da jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, a ranar Litinin a filin wasa na Bata, yayin da ita kuma Zambia za ta fafata da Cape Verde a Ebebiyin. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China