in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Chadi ba ta shakkar Boko Haram, in ji ministan cikin gidan kasar
2015-01-29 10:12:27 cri

Ministan harkokin cikin gidan kasar Chadi Abderahim Bireme Hamid, ya ce, kasar sa ba ta shakkar wani mataki da kungiyar Boko Haram za ta dauka, sakamakon tura sojojin kasar zuwa Kamaru da Najeriya domin yaki da dakarun kungiyar.

Hamid wanda ya bayyyana hakan yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua, ya kara da cewa, dukkanin iyakokin Chadi na da cikakken tsaro, don haka babu wani abun tsoro game da ayyukan Boko Haram.

Ministan ya kara da cewa, ba za a fidda tsammanin yunkurin kai harin ramuwar gayya daga mayakan kungiyar ba, sai dai a daya hannu Chadi ta dauki dukkanin matakan kandagarki, tun ma kafin fara aikewa da sojojin kasar zuwa Kamaru domin yaki da 'yan Boko Haram.

Mr. Hamid ya ce, ana kara tsaurara matakan tsaro a dukkanin wuraren taruwar jama'a, tare da gudanar da bincike, da cafke wadanda ake zaton na da wata alaka da kungiyar a birnin N'Djamena, fadar gwamnatin kasa.

Ministan ya kuma yi kira da jama'ar kasar da su hada kai da mahukunta domin tabbatar da tsaro, da kyakkyawan yanayin zaman lafiya da lumana a fadin kasar baki daya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China