Kazamin fada na ci gaba da gudana tsakanin sojojin Kamaru da na kasar Chadi da mayakan kungiyar Boko Haram ta Najeriya a ranar Lahadi da yamma fiye da sa'o'i uku a Fotokol, wani yankin dake kuriyar arewacin Kamaru dake iyaka da Najeriya, a cewar wasu majiyoyin sojan kasar Kamaru.
Ranar daya ga watan Febrairu, rana ce da ta fi kasancewa cikin rudani ga Boko Haram, wanda bayan wani harin da ta kai da bai ci nasara a muhimmin yankin Maiduguri dake arewa maso gabashin Najeriya, da kuma hare hare ta sama na sojojin kasar Chadi a Gambaru na wannan yankin, dakarun na Boko haram ba su farga ba na kai hare hare a Fotokol dake kasar Kamaru, inda musanyar wuta ta fi kazancewa tun da yammacin ranar, a cewar wasu majiyoyi ba tare da ba da wani adadi ba. (Maman Ada)