in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dole a yaki Boko Haram bisa hadin gwiwar kasa da kasa, in ji AU
2015-01-27 10:55:40 cri

Kungiyar Boko Haram babbar barazana ce ga duniya, kuma ya kamata duniya ta ja daga da ita cikin hadin gwiwa, tare da nahiyar Afrika a sahun gaba bisa kokarin da take bayarwa, in ji Nkosazana Dlamini-Zuma, shugabar kwamitin tarayyar Afrika (AU).

Shugabar ta yi wadannan kalamai a ranar Litinin a yayin bikin bude zaman taron kwamitin zartarwa na kungiyar karo na 26 a birnin Addis Abebe na kasar Habasha.

Ina damuwa sosai kan tashe tashen hankalin da kungiyar Boko Haram ke ci gaba da aikatawa kan al'ummominmu, da sace kananan 'yan mata a cikin makarantunsu, da kona kauyuka, da tsorata al'ummomi gaba daya da kuma kashe mutane haka kawai, in ji madam Dlamini-Zuma. Kungiyar da ake dauka a matsayin wata karamar kungiyar 'yan fashi da makami ta cikin gida, yanzu ta fadada karfinta a yammaci da tsakiyar Afrika. Ya kamata mu tashi tsaye domin murkushe wannan barazana dake karuwa, in ji babbar jami'ar AU.

Kwamitin AU na gaggauta shawarwari a yanzu haka tare da kasashe mambobi da sauran kasashen duniya, da ma abokan hulda kan hanyar da za'a bi wajen yaki da Boko Haram, in ji madam Dlamini-Zuma tare da bayyana cewa, batun Boko Haram, zai kasance cikin jadawalin taron kwamitin sulhu na MDD da na kwamitin tsaron kungiyar AU a yayin zaman tarukan hukumomin biyu da aka tsai da shiryawa a ranakun 30 da 31 ga watan Janairu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China