in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayakan Boko Haram sun kashe mutane 5 a arewancin Nigeria
2015-02-02 11:04:03 cri

Wani wanda aka kai harin a kan idanunsa Musa Ilela ya ce, harin da aka kai a birnin Gombe wanda ake kyautata zato cewar, harin kunar bakin wake ya shafi wata cibiyar bincike dake unguwar Katako.

Musa Ilela ya kara da cewar, shi kuma hari na biyu, an yi niyyar aiwatar da shi ne a kan wata tsohuwar kasuwa.

Ya ce, babu wanda ke da masaniyar musabbabin tashin bam din na tsohuwar kasuwa, to amma mutanen garin suna zargin watakila kungiyar Boko Haram na da hannu a cikin harin da aka kai.

Tun farko wasu mutane 3 da wani soja guda daya sun mutu a yayin da bam ya tashi a cibiyar binciken jama'a ta sojoji.

Hakazalika mutumi na biyu wanda shi ma bam din ya tashi a idanunsa Ibrahim Bello ya ce, mutane 2 ne suka mutu bayan tashin bam din da aka dasa a tsohuwar kasuwa.

Kawo ya zuwa yanzu, shugabannin yankin ba su bayar da wata sanarwa ba a game da harin da aka kaddamar

Tun a ranar Lahadi kungiyar ta Boko Haram ta kaddamar da wasu hare-hare a jihohin Yobe da Borno dake arewa maso gabashin kasar. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China