in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu mutane da ake zargi 'yan Boko Haram sun yi barna a arewacin Nigeria
2015-01-27 11:01:06 cri

Wasu mutane da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kai wani mummunan hari a garin Michika dake jihar Adamawa, wacce ke arewa maso gabashin kasar ta Nigeria

Kamar dai yadda wata majiyar jami'an tsaron kasar ta bayyana, maharan sun kutsa garin na Michika da muggan makamai, a inda suka dinga harbin jama'a ba ji ba gani, suna ta kashe su tare da kona muhallansu, to amma majiyar ta ce, an tura dakarun gwamnati domin dakatar da farmakin wadanda suka kaiwa garin farmaki.

Wata majiya wani shugaban matasan yankin ta bayyana cewar, yawan wadanda suka rasa rayukansu zai yi yawa saboda maharan sun yi muguwar barna kafin zuwan jami'an tsaron.

Mai ba da rahoto na kamfanin dillanci labarai na Xinhua dake jihar ta Adamawa ya yi kokari na gano takamaiman adadin wadanda harin ya shafa, to amma bai samu nasara ba saboda har yanzu jami'an gwamnati ba su ce uffan ba a game da harin da aka kai a garin Michika. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China