in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya jinjina wa IGAD game da rikicin Sudan ta Kudu
2014-11-08 16:57:22 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon ya yaba wa kungiyar shuwagabannin kasashen Gabashin Afirka ta IGAD, bisa namijin kokarin ta, na janyo hankalin sassan Sudan ta Kudu dake rikici zuwa teburin shawara.

Kungiyar ta IGAD dai ta kammala wani taro na yini biyu a birnin Addis Ababan kasar Habasha, inda ta cimma matsayar baiwa sassan kasar Sudan ta Kudun wa'adin kwanaki 15, na ko dai su cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta, ko kuma a kakabawa kasar takunkumi.

A ta bakin kakakin babban magatakardar MDDr, matakin da IGAD din ta dauka ya yi dai dai, zai kuma dace da muradan al'ummar kasar. Kaza lika mista Ban ya yi na'am da aniyar 'yan adawar kasar game da batun rungumar sulhu, tare da kafa gwamnatin hadaka nan da kwanaki 15 masu zuwa.

Daga nan sai ya yi fatan daukacin masu ruwa da tsaki game da rikicin kasar za su kara azamar ganin an kai ga cimma yarjejeniya, wadda za ta ba da cikakkiyar damar daidaitawa, tare da magance tushen matsalar da ke haifar da tashe-tashen hankula a kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China