in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya jajanta game da aukuwar girgizar kasa a kudu maso yammacin kasar Sin
2014-08-04 10:22:36 cri
Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon ya bayyana bakin cikinsa, game da aukuwar girgizar kasar nan da ta fadawa yankin kudu maso yammacin kasar Sin, wadda ta hallaka mutane da dama tare da lalata gine-gine masu yawa.

Cikin wata sanarwar da kakakinsa ya fitar, Mr. Ban ya mika sakon ta'aziyyarsa ga gwamnatin kasar Sin, da kuma iyalan wadanda bala'in ya rutsa da su, yana mai fatan wadanda suka jikkata za su murmure cikin sauri.

Ya ce MDD a shirye take ta tallafi duk wani shiri na bada tallafin jin kai, da samar da taimakon kasa da kasa a duk lokacin da bukatar hakan ta bijiro. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China