Dieye zai maye gurbin Tegegnework Gettu wanda shi ma ya kama sabon aikinsa a matsayin mataimakin sakatare janar kan babban taro da gudanar da tarukan MDD, in ji sanarwar.
Dieye ya hau wannan mukami ne dauke da dimbin nasarori da ya cimma a baya a karkashin shirin na UNDP, wadanda suka hada da kasancewa kan mukamin shugaban ma'aikata da kuma darektan ofishin zartaswa.
Kafin a nada shi kan wannan matsayi, Dieye ya hau mukamin mataimakin darektan yanki, a yankin kasashen larabawa, da birnin New York, da kula da shirye-shiryen UNDP a arewacin Afirka, yankin gabas ta tsakiya da kuma na kasashen yankin Gulf. (Lami)