Ban ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa ta hannun kakakinsa, inda ya bukaci da a gudanar da bincike na musamman dangane da yankurin juyin mulkin da wasu sojoji suka yi a kasar ranar 30 ga watan Disamba da bai yi nasara ba.
Sanarwar ta kuma yi kira ga gwamnatin kasar ta Gambia da dakarunta na tsaro da su gudanar da ayyukansu bisa la'akari da kare hakkin bil-adama. Ya kuma nanata akidar MDD na yin allawadai da duk wani yukurin kwace mulki ta hanyar da ta sabawa doka.
A ranar Talata ce aka yi yunkurin kifar da gwamnatin Yahya Jammeh na Gambia, bayan da aka rika jin harbe-harbe a Banjul, babban binrin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu sojoji 5 baya ga wasu da dama aka kama.
Rahotanni na cewa, yanzu dai shugaba Jammeh ya dawo kasar bayan wani bulagura da ya yi tare da iyalansa zuwa Dubai a makon da ya gabata. (Ibrahim)