Hong Lei yayi bayanin cewa wannan ziyara ta zo ne bisa gayyatar takwarorinsa na wadannan kasashen da suka hada da ministar harkokin waje da cinikayya da kasashen waje ta Kenya Amina Mohamed, da ministan harkokin waje na Sudan Ali Ahmed Kurti, da ministan hulda da kasashen waje na Kamaru Pierre Moukoko Mbonjo, Sauran sun hada da ministan harkokin waje da hadin gwiwa na Equatorial Guinea Agapito Mba Mokuy, da ministan harkokin waje da hadin gwiwa da kasashen waje na Kongo Kinshasa Raymond Tshibanda.
Hong Lei ya ce, tun daga shekarar 1991 zuwa yanzu, ministan harkokin waje na Sin ya kan kai ziyarar sa ta farko a kasashen Afirka a kowace shekara, abinda ya bayyana muhimmancin da Sin ta dora kan kasashen Afirka.
Yayi bayanin cewa makasudin ziyarar minista Wang a wannan karo shi ne tabbatar da ra'ayin taron ayyukan shafar kasashen waje, da tabbatar da sakamakon da aka samu bisa ziyarar shugaban kasar Sin da firaministan kasar a nahiyar Afirka, tare da sada zumunci da kara amincewa da juna da sa kaimi ga hadin gwiwa, a kokarin sa kaimi ga bunkasa dangantaka tsakaninsu zuwa wani sabon mataki.(Fatima)