in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Algeria ta yi alkawarin taimakawa wajen warware rikicin kasar Libiya
2014-12-21 17:05:04 cri
Mahukuntan kasar Algeria sun jaddada aniyar taimakawa yunkurin da ake yi, na shawo kan rikicin siyasa da ya dabaibaye kasar Libiya.

Kamfanin dillancin labaru na APS, ya rawaito mataimakin ministan harkokin wajen kasar ta Algeria Abdelkader Messahel, na cewa kasar sa za ta hada kai da daukacin masu ruwa da tsaki, wadanda ke da burin ganin an kawo karshen tashe-tashen hankula a kasar ta Libiya.

Messahel ya ce al'ummar Libiyan ne suka fi kowa sanin hanyoyin da suka dace a bi, wajen warware matsalar kasar, don haka babu wata kasa ta daban, da za ta tsoma hannu cikin wannan sha'ani. A cewar sa Aljeriya na da burin ganin an aiwatar da kudurin kwamitin tsaron MDD, da ya shafi gudanar da sulhu da dawoda yanayin zaman lafiya da lumana a Libiya.

Messahel ya kara da cewa ya yin da ake kokarin aiwatar da matakan warware rikicin kasar ta Libiya, dole ne a maida hankali ga batun yaki da 'yan ta'adda, da kare martaba da 'yancin kasar, tare da bin hanyoyin sake ginin kasar bisa tsari na dimokaradiyya.

Libiya dai na fuskantar karin matsaloli baya ga na siyasa, ciki hadda yawaitar kwararar magoya bayan kungiyoyin masu tsattsuran ra'ayi, da na masu fataucin miyagun kwayoyi, da kuma masu safarar makamai, lamarin da baya rasa nasaba, da yaduwar tashe-tashen hankula a Arewacin Mali da kuma wasu sassan kasar Libiyan.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China