in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci shugabannin Sudan ta Kudu da su martaba yarjejeniyar Arusha
2015-01-23 10:00:22 cri

Shugabannin kasashen Afirka sun yi kira ga jagororin bangaren adawar Sudan ta Kudu da su mutunta yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a Arushan kasar Tanzaniya.

Shugabannin, ciki har da shugaban kasar Tanzaniya Jakaya Kikwete sun yi wannan kiran ne ranar Laraba a birnin Arusha da ke arewacin kasar Tanzaniya jim kadan bayan da shugabannin Sudan suka ce, rashin mutunta yarjejeniyar ta Arusha ce, dalilin rashin kawo karshen fadan da aka dade ana fama da shi a wannan jaririyar kasa.

Don haka shugaban kasar Tanzaniya, kana babban mai shiga tsakani a wannan rikici, ya bukaci shugabannin da ke fada da juna, da su aiwatar da dukkan tanade-tanaden da ke cikin yarjejeniyar.

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar dai sun sanya hannu kan yarjejeniyar ta Arusha ce, da nufin hada kan bangarorin SPLM da ke gaba da juna. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China