in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin kasar Sin ya baiwa ma'aikata 'yan kasar Kenya lambobin yabo bisa kwazonsu
2014-12-24 15:45:32 cri

A jiya Talata 23 ga watan nan ne ofishin kula da harkokin kasar Kenya, na kamfanin shimfida hanyoyi da gadoji (CRBC) na kasar Sin, ya shirya wani biki a Nairobi babban birnin kasar, domin ba da lambar yabo ga ma'aikatan da suka dade suna baiwa kamfanin gudummawa. Ya yin wannan biki an karrama ma'aikata 'yan kasar Kenya 90, tare da ma'aikata Sinawa 8 da lambobin yabo.

Rahotanni sun bayyana cewa cikin wadannan ma'aikata da suka samu lambobin yabo, 92 daga cikinsu sun dade suna aiki a kamfanin na CRBC mallakar kasar Sin, wanda ke ayyukan shimfida hanyoyi, da gadoji, inda suka kwashe fiye da shekaru 10 suna baiwa kamfanin hidima, sai kuma shida daga cikinsu, wadanda suka shafe shekaru fiye da 21, cikin su hadda wanda ya zarce shekaru 28 yana yiwa kamfanin aiki.

A yayin bikin ba da lambar yabon, babban manajan ofishin kula da harkokin Kenya na kamfanin Li Qiang, ya taya wadannan ma'aikata murnar samun lambobin yabon. Ya ce,

"A madadin kamfanin CRBC, ina taya wadannan ma'aikata da suka samu lambobin yabo murna sakamakon gudummawar da suka dade su na baiwa kamfaninmu. Nasarorin da kamfanin CRBC ya samu a kasar Kenya, na da nasaba da kokarin da kuke yi, da kuma kwarewa da kuke nuna wajen aiki. Tabbas za mu nuna gamsuwa, da kuma godiya ga gudummawar da kuke bayarwa ga kamfaninmu."

Shekarar da muke ciki shekara ce ta cika shekaru 30 da kafuwar kamfanin CRBC a kasar Kenya. Kuma kawo yanzu akwai ma'aikata 'yan kasar Kenya 10,160 a wannan kamfani, wadanda kuma yawansu ya kai kashi 90 cikin kashi dari na daukacin ma'aikatan kamfanin. A cikin wannan adadi akwai mutum 178 da suka dade su na aiki a kamfanin har fiye da shekaru 10. Domin nuna godiyarsa gare su ne, da kuma karfafa gwiwar sauran ma'aikatan, ofishin ya tsara bada lambobin yabo a shekarar 2010, don bai wa wadanda suka dade suna aiki a kamfanin, bikin da ake ci gaba da gudanarwa bayan shekaru biyu biyu.

Wani ma'aikaci dan kasar ta Kenya wanda ya samu lambar yabon, ya furta cewa, a matayinsa na ma'aikacin kamfanin CRBC tsawon fiye da shekaru 10, abin da ya kamata ya yi shi ne, zama abin koyi ga sauran sabbin ma'aikata, a kokarin inganta martabar kamfanin. Ya kara da cewa,

"Mun fi nuna sanin-ya-kamata in an kwatanta da sabbin ma'aikata a wasu fannoni. Wadannan matasa suna mai da hankulansu kan abubuwan da muka fada ko muka aikata, hakan ya sa muke da alhakin sanya ido kansu, da zama abin koyi gare su, domin magance aukuwar wani abu da ka iya yin illa ga kamfaninmu."

Han Chunlin, mashawarcin jakada ne kan aikin kasuwanci, na ofishin jakadancin kasar Sin da ke Kenya, a yayin bikin ya bayyana cewa, ko shakka babu ma'aikatan da suka samu lambobin yabon jari ne ga kamfanin na CRBC. Ko da yaushe ofishin jakadancin na Sin ya kan jaddada muhimmancin daukar nauyin kula da mazauna wurin, dake wuyan kamfanonin na Sin yayin da suke kokarin gudanar da ayyukansu. Ya ce,

"Ko da yaushe mu na karfafa gwiwar dukkanin kamfanonin kasar Sin, wajen sauke nauyin da ke wuyansu a fannin kula da jama'ar kasar da suke ciki, kamar batun samar da guraban ayyukan yi ga mazauna wurin, da kara yawan mazauna wurin masu gudanar da harkokin kamfanoni, gami da sanar wa ma'aikatansu burin ci gaba a kamfanonin. Idan har kamfani ya na da aniyar raya ayyukansa a duk fadin duniya, ba shakka ya dace ya kara kwazo wajen mayar da kamfani kan turbar da ta dace da yanayin wurin, a matsayin daya daga manyan tsare-tsaren sa."

An labarta cewa, wannan kamfani na CRBC shi ne zai gudanar da aikin shimfida layin dogo daga Mombasa zuwa Nairobi, wanda aka kaddamar da shi ba da jimawa ba, mai tsahon kilomita 480, wanda kuma za a shimfida bisa ma'aunin kasar Sin na ajin farko.

Kaza lika an kiyasta cewa, aikin zai samar da guraban ayyukan yi kusan dubu 30 ga jama'ar Kenya, a fannonin sarrafa injuna, da gwaje-gwaje, da safiyo, da gyara na'urori, da kuma aikin gudanarwa. Bugu da kari, ana sa ran ganin ma'aikata 'yan kasar Kenya masu yawa cikin ayyukan da kamfanin na CRBC zai gudanar cikin shekaru 20 masu zuwa.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China