in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bada lambar yabo ga tawagar 'yan sandan Sin dake kasar Liberia
2015-01-23 15:18:09 cri
Tawagar musamman ta MDD dake kasar Liberia wato UNMIL, ta gudanar da bikin bada lambar yabo ga tawaga ta biyu ta 'yan sandan kasar Sin masu aikin kiyaye zaman lafiya a kasar.

Yayin bikin karrama wadannan jami'ai da ya gudana jiya Laraba, an yabawa 'yan sandan kasar ta Sin su 140, bisa irin gudummawar da suke bayarwa, wajen tabbatar da zaman lafiya musamman lokacin barkewar cutar Ebola a kasar.

Babban direkta mai lura da harkar 'yan sanda na UNMIL Gregory Hinds na daya daga halarta bikin mika lambobin yabon.

Wannan dai biki ya biyo bayan umurnin da mataimakin babban sakataren MDD mai kula da harkokin kiyaye zaman lafiya Hervé Ladsous ya bayar ne, inda MDD ta godewa daukacin mambobin tawagar 'yan sandan kiyaye zaman lafiya na kasar Sin dake kasar ta Liberia, bisa jaruntarsu, da kwazo yayin da ake fuskantar cutar Ebola.

Ya kuma kara da cewa,'yan sandan sun kuma gudanar da ayyuka masu yawa yadda ya kamata, baya ga kokarin su na tabbatar da zaman lafiya da lumana a kasar ta Liberia. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China