in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Barca ta taka rawar gani a wasan da ta doke Atletico Madrid
2015-01-15 14:37:22 cri
Kulaf din FC Barcelona karkashin jagorancin koci Luis Enrique, ya samu wata nasara a wasan sa da Atletico Madrid na ranar Lahadi, wasan da Barcelona ta lashe da 3 da 1 a filin wasa na Camp Nou.

Barca ta buga wasan na Lahadi bayan da ta rasa nasara a wasan ta da Atletico har karo 6 a baya. Ya yin da kuma a daya hannun kulaf din ke shan suka daga bangarori daban daban, da ma batun yiwuwar korar kocin kunhiyar in ba don nasarar da suka samu a wannan wasa na karshen mako ba.

Ko da yake Xabi Hernandez na Barca bai buga wasan ba, kocin kungiyar Enrique ya dora nauyin nasarar wasan ga Leo Messi, da Neymar da kuma Luis Suarez a gaba, ya yin da Ivan Rakitic, da Busquets da Andres Iniesta suka taka leda a tsakiyar fili.

Manazarta dai na ganin Barca ta taka muhimmiyar rawa wajen lashe wasan nan na karshen mako a gaban dubban 'yan kallo. Neymar na Brazil ne dai ya fara bude ragar Atletico a minti na 12. Sai kuma kwallon da ake tantama a kanta wadda Barca ta samu ta hannun Suarez, wadda wasu ke gani Messi ya taba da hannu kafin mikawa Suarez.

Bayan dawowa hutun rabin lokaci ne kuma Messi ya yiwa dan wasan Atletico keta, inda nan take alkalin wasan ya bada bugun daga kai sai mai tsaron gida, ba kuma tare da bata lokaci ba Mario Mandzukic ya jefa kwallo daya tilo da Atletico ta ci a zaren Barca. Wanna dai shi ne karon farko da Messi ya janyowa kulaf din sa bugun daga kai sai mai tsaron gida a daukacin lokacin da ya shafe yana taka leda.

Haka dai aka yi ta dauki ba dadi, har lokacin da Messi ya karkare sakamakon wasan da kwallo ta 3.

Sakamakon wannan wasa dai ya sanya Barca kasancewa ta biyu a teburin La Liga, inda take biye da Real Madrid dake matsayin farko nasarar da ko shakka babu ta yi matukar faranta ran kocin ta Enrique.(Saminu Alhassan Usman)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China