in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rogers ya ce abu ne mai matukar wuya a iya maye gurbin Gerrard
2015-01-08 15:16:29 cri
Babban manajan kulaf din Liverpool Brendan Rodgers, ya ce abu ne mai matukar wuya a samu dan wasan da zai iya maye gurbin Steven Gerrard.

Rogers ya bayyana hakan ne bayan da Gerrard din ya tabbatar da aniyar sa ta barin Liverpool.

Rogers ya ce farkon zuwan sa kulaf din na Liverpool a shekarar 2012, ya tabbatar da kwarewar Gerrard, ya kuma yi imanin dan wasan zai iya ci gaba da baiwa kungiyar karin gudummawa. A kuma wannan lokaci ne ya hakikance irin tasirin dan wasan, wajen sauya alkiblar kungiyar ta hanyar samun karin nasarori.

"Dole ne ka san cewa wata rana zai so barin mu, kuma dole ka nemi wasu da za su maye gurbin sa, wannan kuma shi ne abinda muke dubawa. Kusan abu ne mawuyaci a samu dan wasan da zai iya maye gurbin Gerrard a fannin kwarewa, amma duk da haka zamu ci gaba da nema. Steven Gerrard dan wasa ne na musamman, amma kamar yadda tarihin kwallo ya nuna, a koda yaushe akwai dama ga 'yan wasa masu tasowa", a kalaman Rogers. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China