MDD ta ba da lambar yabo na zaman lafiya ga jami'an tsaro na kiyaye zaman lafiya na Sin a Liberiya
A jiya Talata 20 ga wata, a madadin MDD, tawagar musamman ta MDD a Liberiya ta ba da lambobin yabo na zaman lafiya ga jami'an tsaro na kiyaye zaman lafiya na Sin a kasar 140, domin yaba musu a kokarin su wajen ba da babbar gudummawa a ayyukan tabbatar da zaman lafiya.
A watan Yuni na bara, tun bayan da wadannan jami'an tsaro na Sin a Liberiya sun shiga yankin ayyuka da MDD ta kebe, sun kammala ayyukansu lami lafiya irin na yin sintiri, da bincike da sauransu, a saboda haka, suka samu yabo sosai daga wajen ofishin jakadancin Sin a Liberiya da mazauna wurin.(Fatima)