Baki daya, rundunar sojan kiyaye zaman lafiya na Sin a Liberiya karo na 17 tana kunshe da sojoji 558, wadanda za su gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya a Liberiya har tsawon watanni 8.
Sin tana gudanar aikin kiyaye zaman lafiya a Liberiya bisa kuduri mai lamba 1509 da kwamitin sulhu na MDD ya zartas. Ta fara wannan aiki ne a watan Disamba na shekarar 2003. A kullum a kan canza sojoji a watanni takwas takwas, kuma wannan ne karo na 16 da aka canza sojojin Sin dake Liberiya.(Fatima)