Bisa rahoton da wata kungiyar jin dadin jama'a ta duniya mai suna "Oxfam International" ta bayar jiya Litinin ranar 19 ga wata, an ce, muddin ba a magance ci gaba da matsalar rashin daidaito ba, ya zuwa shekara ta 2016, mai yiwuwa ne yawan dukiyoyin da kashi 1 cikin 100 na attajirai na duniya ke mallaka zai zarce wanda sauran al'ummar duniya da yawansu ya kai kashi 99 cikin dari ke mallaka gaba daya.
Madam Winnie Byanyima, babbar sakatariyar kungiyar Oxfam International mai hedkwata a kasar Birtaniya ta furta cewa, a matsayinta ta shugabar taron shekara-shekara ta Davos na dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya na shekarar 2015, za ta yi kira da a dauki matakai don kawo karshen matsalar rashin samun daidaito a tsakanin mutane, da yaki da masana'antu masu zambar haraji, gami da sa kaimi ga aikin daddale yarjejeniya kan matsalar yanayi ta duniya.(Kande Gao)