in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai haske a gaba ma tattalin arzikin Afrika bayan koma bayan matsalolin daya fuskanta a shekarar 2014
2014-12-24 20:43:16 cri
Tattalin arzikin Afrika yana da haske a gaban shi bayan koma bayanwasu matsalolin da y a fuskanta a shekarar nan mai karewa na 2014.

Kamar yadda Edith Togba,wata malamar tattalin arziki a jami'ar Alassane Ouattara dake Boiake, a tsakiyar kasar Kwadibuwa ta shaida ma wakilin kamfanin dillanci labarai na kasar Sin Xinhua cikin hirar da ta yi da shi.

Daya daga cikin koma bayanmatsalolin da tattalin arzikin ya fuskanta shi ne annobar Ebola wanda wadda yayi matukar shafar kasashen dake yammacin nahiyar.

Baya ga Ebola inji Malama Edith Togba, kasashen Afrika sun kuma fuskanci wassu kalubaloli da suka hada da rashin tabbas na al'ammurran siyasa, cin hanci da sauran abin da ya jibanci hakan.

Masaniyar tattalin arzikin ta lura da cewa tattalin arzikin afrika Afrika zai fuskanci kalubale a shekara mai kamawa ganin yadda yawancin kasashen zasu aiwatar da babban zaben su abinda ke tsoratar da masu zuba jari saboda tashin hankalin da kan biyo baya a kasashe da dama.

Amma ganin yadda ake ayyukan inganta tattalin arziki mai karfi, Madam Togba tana sa ran samun cigaba mai kyau.

Game da kasashen da suka taka rawar gani a shekarar 2013 da shekarar 2014, Togba ta lissafa kasashen Saliyo da Chadi da Kwadibuwa da suka samu har kashi 9,.6%, kashi 9.5% da kashi 9.3% na cigaban tattalin arzikin su.

Ta jinjina ma huldar dake tsakanin kasar Sin da nahiyar Afrika tana mai nuni da cewa a cikin 'yan shekarun nan kasar Sin ta samar da kayayyakin more rayuwa a kasashen Afrika kamar Kwadibuwa, Guinea, Uganda da Kamaru.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China