Kana an sanar da cewa, hukumomin da ke halartar taron da gwamnatin Abu Dhabi sun zuba jari da samar da rancen kudi zagaye na biyu ga kasashe masu tasowa don gudanar da ayyuka biyar game da makamashin da za a iya sake yin amfani da su.
Rahoton ya yi nuni da cewa, yawan kudin da ake kashewa kan makamashin da za a iya sake yin amfani da su bai kai na makamashin kwal ko iskar gas a yankuna da dama na duniya ba. Rahoton ya bayyana cewa, sakamakon faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya da rashin kudin tallafi, makamashi na tsirrai, iska, ruwa ko na zafin kasa suna da fifiko, kudin da ake kashewa wajen samar da wutar lantarki ta wadannan makamashi bai kai na kwal ko man fetur ko iskar gas ba. (Zainab)