Daruruwan masu rajin kare hakkin bil adama ne suka yi zanga-zanga ranar Talata a gundumar Tamenrasset dake kasar Aljeriya, don nuna fushinsu kan shawarar gwamnatin kasar ta fara aikin hako gas a yankin Shale.
Bayanai na nuna cewa, tun a ranar Lahadi ne galibin mazauna yankunan Ain Salah da Tamenrasset suke yin bore da maci a wani mataki na dakatar da kamfanin hakar iskar gas na Sonatrach daga fara aikin hako gas a yankin Shale.
Daya daga cikin masu shirya boren daga yankin na Ain Salah mai suna Abdelkarin Ouanilli ya ce, aikin ba abin da zai haifar illa kawo matsala ga lafiyar mazauna yankunan da kuma muhalli. Don haka suka ce ba za su dakatar da boren da suke ba, har sai gwamnati ta cika musu bukatunsu, ciki har da dakatar da aikin hako gas din, janye dukkan na'urorin da aka jibe a wuraren da ake son hako wannan gas.
A watan Yuni ne shugaba Abdelaziz Bouteflika ya ba da umarnin fara aikin hako gas din a yankin Shale, inda ya umarci hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da cewa, aikin bai kawo illa ga albarkatun ruwa da kuma muhalli ba.(Ibrahim)