in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawaga ta 2 ta likitocin Sin dake kasar Saliyo ta mika ayyuka ga tawaga ta uku
2015-01-19 11:03:07 cri
An gudanar da bikin mika ayyukan tawaga ta biyu, ta likitocin kasar Sin dake kasar Saliyo, zuwa tawaga ta uku a ranar 18 ga watan nan.

Ya yin bikin da ya gudana a jiya Lahadi a sansanin tawagar, an gabatar da yadda za a gudanar da ayyuka na gaba, ciki hadda tsarin sauke nauyin ayyukan, da yawan abubuwan da ake amfani da su, da wadanda aka tanada da dai sauransu.

Bisa shirin da aka tsara, dukkan mambobin tawagar ta biyu za su koma gida Sin a ranar 20 ga watan nan.

A ranar 17 ga watan nan ne dai rukunin farko na tawaga ta uku ta kasar Sin dake kasar Saliyo, ya isa asibitin sada zumunta tsakanin Sin da Saliyo, dake wajen birnin Freetown na kasar Saliyo, inda suka gana tare da jami'an bangaren kasar ta Saliyo. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China