in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shekaru 6 a jere yawan motocin da Sin ta samar ya kasance a matsayin koli a duniya
2015-01-13 14:13:11 cri
Kungiyar masana'antun motoci ta kasar Sin ta bayyana cewa, yawan motocin da Sin ta samar a shekarar 2014 ya kai miliyan 23 da dubu 720, adadin da ya karu da kashi 7.3 cikin dari bisa na shekarar 2013, yayin da yawan motocin da kasar ta sayar a baran ya kai miliyan 23 da dubu 490, adadin da shi ma ya karu da kashi 6.9 cikin dari bisa na 2013.

Bisa kididdigar kungiyar ta ce wannan adadi ya kai matsayin koli a duniya cikin shekaru 6 a jere.

A sakamakon hakan, gwamnatin kasar Sin ta jinjinawa fannin kera motoci masu amfani da sabbin makamashi, da yadda kamfanonin suke kara samar da motoci masu inganci, da ma yadda al'ummar kasar ke kara amincewa da motoci masu amfani da sabbin makamashi.

Rahotanni na nuna cewa an samun ci gaba cikin sauri, game da sha'anin kirar motoci masu amfani da sabbin makamashi a shekarar ta bara, inda yawan irin wadannan motoci a shekarar ya kai dubu 75, adadin da ya rubanya sama da sau uku bisa na shekarar 2013. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China