Sha'anin kera motoci masu amfani da makamashin wutar lantarki na kasar Sin zai kasance a kan gaba a duniya
Bisa labarin da kungiyar masana'antun kera motoci ta kasar Sin ta bayar a ranar 10 ga wata, an ce, yawan motoci masu yin amfani da sabbin makamashi da Sin ta kera a watanni 11 na farkon shekarar bana ya kai 57125, yayin da aka sayar da motoci 52944 daga cikinsu. Ana sa ran cewa, a bisa jagorancin manufofin kasar da kokarin da al'ummar kasar ta yi, sha'anin kera motoci masu yin amfani da wutar lantarki na kasar Sin wanda ya zama daya daga cikin sabbin makamashin da motoci ke amfani da shi zai kasance a kan gaba a duniya a nan gaba.
Masana sun bayyana cewa, shekarar 2014 ita ce shekara ta farko da aka gabatar da motoci masu yin amfani da sabbin makamashi ga jama'a. A nan gaba, yayin da aka samu kyautatuwar kayayyakin more rayuwa da saukin sayen motocin da manufofin dake shafar wannan fanni, kasar Sin za ta cimma burinta na sayar da motoci masu yin amfani da wutar lantarki dubu 500 a shekarar 2016. (Zainab)