Bisa labarin da aka bayar, an ce, ya zuwa karshen shekarar 2013, yawan fasinjojin da jiragen saman kasar Sin suka dauka ya kai matsayi na biyu a duniya a shekaru 9 a jere, wadda ta kasance kasa ta biyu a harkar jigilar jiragen sama a duniya, kana ingancin matakan tsaron jiragen saman kasar Sin yana kan gaba a duniya. Yawan filayen jiragen sama a kasar Sin ya kai 198, kuma yawan jiragen sama da Sin ta mallaka ya kai 3664, yayin da yawan hanyoyin jiragen sama da aka bude a tsakanin Sin da sauran kasashen waje ya kai 427, wadanda suke iya hada kasar Sin da birane 118 na kasashe 50 na duniya. (Zainab)