Kididdigar ta kuma nuna cewa, farashin abinci ya karu da kashi 2.9 cikin dari bisa na shekarar 2013, adadin da ya kai kashi 0.95 cikin dari bisa na daukacin CPI din a dukkan fannoni.
Haka zalika, farashin wasu kayayyakin da ba na abinci ba iri 5 ya karu, yayin da na wasu iri biyu ya ragu. Daga cikinsu, yawan karuwar farashin tufaffi, da fannin kiwon lafiya, da kayayyakin amfanin yau da kullum, da na'urorin amfani a gidaje, da kuma hidimar gyare-gyare yana kan gaba.
Ban da wannan, a sakamakon faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya, farashin kayayyakin da kamfanoni suke fitarwa wato PPI ya ragu a watan Disambar shekarar ta 2014 da kashi 3.3 cikin dari. Yayin da kuma yawansa a dukkanin shekarar 2014 ya ragu, da kashi 1.9 cikin dari. (Zainab)