in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya kai ziyararsa ta farko a nahiyar Afirka a cikin sabuwar shekara
2015-01-12 16:08:32 cri

Daga ranar 10 zuwa 11 ga watan da muke ciki ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya kai ziyarar aiki a kasar Kenya, a matsayin zangon farko na rangadin da yake kai wa a wasu kasashen dake nahiyar Afirka a wannan sabuwar shekara. A yayin ziyararsa, Wang Yi ya yi shawarwari na keke da keke tare da shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta kan wasu muhimman batutuwa da dama, kana ya tattauna tare da takwararsa ta kasar Kenya Amina Mohamed kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, tare da daddale takardar fahimtar juna game da kafa kwamitin hadin gwiwa da bada jagoranci a tsakanin kasashensu, inda Wang Yi ya bayyana kwarin gwiwarsu kan dangantakar dake tsakanin Sin da Kenya.

Tun daga shekarar 1991 har zuwa wannan lokaci, ministan harkokin wajen kasar Sin ya cigaba da zaben kasashen dake nahiyar Afirka a a matsayin zangon farko wajen kai ziyarar aiki a kasashen ketare a cikin sabuwar shekara, wannan ne ya kasance dadadar al'adar da kasar ke bi wajen harkokinta diplomasiyya. Game da wannan, mista Wang Yi ya bayyana cewa, yin shawarwari tare da abokanmu na kasashen Afirka ya kasance muhimmin mataki wajen sada zumunta, da gudanar da hadin kai, da kuma neman ci gaba tare, dukkansu sun bayyana cewa kasar Sin tana mai da kasashen Afirka a wani muhimmin matsayi kan harkokinta na diplomasiya, kuma jama'ar kasar Sin suna daukar jama'ar kasashen Afirka a wani babban matsayi. Game da burinsa na kai ziyara a kasashen Afrika a shekarar bana, Wang Yi ya ce,

"Da farko za mu bi manufar sahihanci da shugabanmu Xi Jinping ya gabatar game da kasashen Afirka, da kuma inganta shawarar da firaminista Li Keqiang ya gabatar a yayin ziyararsa a kasashen Afirka a shekarar bara. Kana za mu tabbatar da jerin ra'ayoyin bai daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma a lokacin ziyarar da suka kai wa juna, da muhimman yarjejeniyoyin da suka daddale. Bayan haka kuma, za mu share fage kan taron ministoci karo na 6 na dandalin tattaunawar hadin kan kasashen Afirka da Sin da za a shirya shekarar bana a kasar Afirka ta kuduKudu, domin mai da hankali kan ra'ayoyi da shawarwarin abokanmu na kasashen Afirka."

A yayin da yake ganawa da wakilinmu na CRI, Wang Yi ya nuna cewa, kasar Sin na fatan amfani da kyakkyawar dadadar dangantaka a tsakanin Sin da Kenya don inganta hadin kai a tsakanin bangarorin biyu. Game da dalilin da ya sa kasar Sin ke kokarin taimaka wa kasashen Afirka wajen shimfida hanyar dogo, da gina hanyoyin mota, da kuma zirga-zirgar jiragen sama, haka kuma me ya sa kasar Sin ta zuba jari kan hanyar layin dogo a tsakanin biranen Monbasa da Nairobi na kasar Kenya? Wang Yi ya amsa cewa, hadin kai tsakanin Sin da Kenya hadin kai ne irin na samun moriyar juna dake tsakanin kasashe masu tasowa. Yanzu kasar Kenya na bukatar bunkasa muhimman kayayyakin more rayuwa, a matsayinta na wata aminiyar kasar Sin dake fatan bayar da nata taimako. Bayan haka kuma, wannan hanyar layin dogo ta Monbasa da Nairobi wata nasara ce da aka tabbatar bisa ra'ayin bai daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma game da raya tsarin hanyoyin dogo na kasashen Afirka, kasar Sin na fatan karfafa kokarinta na cimma wannan buri. Wang Yi ya ce,

"A yayin da firaminista Li Keqiang ya kai ziyara a hedkwatar kungiyar tarayyar kasashen Afirka wato AU a shekarar da ta wuce, shugabar kungiyar dokta Nkosazana Dlamini Zuma ta bayyana mana burin jama'ar Afirka, wato hada kan dukkan kasashen Afirka ta hanyoyin dogo. A matsayin abokiyar kasashen Afirka, muna son yin kokari domin taimaka musu wajen cimma wannan burin. Gaskiya wannan babban aiki ne, akwai bukatar mu tsara shiri daga dukkan fannoni, da kuma inganta shi sannu a hankali. Muna da imanin cewa, ta hanyar kokarin da muke yi tare, tabbas ne za a cimma wannan buri."

A nata bangare, ministar harkokin wajen kasar Kenya madam Amina Mohamed ta bayyana cewa, tana fatan ziyarar da mista Wang Yi ya kawo a kasarta za ta samar da sabon kuzari ga hadin kan bangarorin biyu a fannoni daban daban. Ta ce,

" Wannan ziyara ta nuna cewa, kasashen Kenya da Sin na da zumunci cikin dogon lokaci, suna kuma nuna amincewa da juna a fannin siyasa. Kasar Sin tana mayar da hankali sosai kan bunkasa dangantakar dake tsakaninta da kasashen Afirka, ciki har da Kenya, bangarorin biyu za su karfafa hadin kai kan muhimman batutuwan da ke shafar babbar moriyarsu, kana da kara ianganta dangantakar abokantaka ta hadin kai cikin daidaici irin ta samun moriyar juna da cimma nasara tare, da nufin ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen Kenya da Sin zuwa wani sabon matsayi." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China