in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana mai da hankali kan tattalin arziki da tsaro yayin da ake hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka
2015-01-14 16:52:55 cri

A ranar 10 ga watan Janairu, mista Wang Yi ministan harkokin wajen kasar Sin, ya fara ziyararsa ta farko a shekarar 2015, wadda ta kai shi zuwa kasashe 5 dake nahiyar Afirka, wato Kenya, Sudan, Kamaru, Equatoria Guinea, da Congo Kinshasa. A cewar Madam He Wenping, shahararriyar masaniya kuma mai bincike kan harkokin Afirka ta kasar Sin, ziyarar ta bayyana yadda bangaren Sin da kasashen Afirka suke dangantakar kut da kut.

'Har kullum kasar Sin tana kallon nahiyar Afirka a matsayin babban tushen aikinta na hulda da kasashen waje. Saboda kokarin habaka hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa ya kasance daya daga cikin manyan manufofin kasar Sin ta fuskar diplomasiya, hakan ya sa kokarin hadin kai tare da kasashen Afirka ya zama wani babban wajibi ga kasar Sin, ta la'akari da yadda aka fi samun kasashe masu tasowa a nahiyar Afirka.'

A shekarun baya, huldar dake tsakanin Sin da Afirka ta samu ci gaba sosai, musamman a fannin tattalin arziki da cinikayya. Alkaluma sun shaida cewa, yawan kudin ciniki tsakanin bangarorin 2 ya kai kimanin dala biliyan 10 a shekarar 2000, jimilar da ta zarce dala biliyan 200 a shekarar 2014. Haka zalika, yawan kudin da kasar Sin ta zuba ma kasashen Afrika shi ma ya karu daga dala miliyan 500 na shekarar 2000 zuwa kimanin dala biliyan 30 a shekarar bara, wanda saurin karuwarsa yake wuce kashi 20% a ko wace shekara.

Ban da haka kuma, don kara habaka hadin gwiwar da ake samu tsakanin Sin da Afirka, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da manufar da ake bi a kokarin hulda da kasashen Afirka, wato 'bin gaskiya, daukar nagartattun matakai, kulla abokantaka, da nuna sahihanci', a yayin ziyararsa a nahiyar Afirka a shekarar 2013. Sa'an nan a nasa bangaren, firaministan kasar Sin mista Li Keqiang shi ma ya gabatar da wasu shawarwari don karfafa hadin gwiwar da ake yi tsakanin Sin da Afirka. Dangane da shawarwarin, madam He Wenping ta ce sun kasance manyan shirye-shiryen da aka tsara don gina ababen more rayuwa a daukacin nahiyar Afirka, wadanda za su taimakawa kasashen Afirka raya tattalin arzikinsu yadda ya kamata.

Za a ma iyar ganin wadannan manufofin kasar Sin bisa la'akari da shawarwarin da ministan wajen kasar Sin Wang Yi ya yi tare da shugabannin wasu kasashen da ya kai ziyara. Ga misali, yayin hirarsa tare da takwararsa ta kasar Kenya, minista Wang ya ce, kasar Sin za ta yi kokarin habaka hadin kai tare da kasar Kenya musamman ma a fannonin aikin gona, raya ababen more rayuwa, kiyaye muhalli da halittu, makamashi mai tsabta, da dai makamantansu. Dangane da haka, Madam He ta ce, yanzu kasar Sin ta fi mai da hankali kan yanayin musamman da wata kasa take ciki da abin da ake bukata, yayin da take hadin kai da wata kasar nahiyar Afirka.

'Da ma mun fi mai da hankali kan tattalin arziki, da ziyarar shugabanni, sa'an nan sannu a hankali mun fara lura da cudanyar al'adu, hadin gwiwa a fannin kimiyya da fasaha, gami da kiyaye muhalli. Ban da haka kuma, hadin gwiwar da ake yi tare da kasashe daban daban ta kan sheda wasu yanayin da suka sha bamban da juna.'

Haka zalika, wani abin da ya dace a sa lura kansa shi ne, yayin ziyararsa a wannan karo mista Wang Yi ya halarci taron shawarwari na nuna goyon baya ga kungiyar IGAD tare da sulhunta bangarorin dake gaba da juna a kasar Sudan ta Kudu. Wannan lamarin ya nuna yadda kasar Sin take dukufa wajen taka muhimmiyar rawa a kokarin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a nahiyar Afirka. Yanzu kasar Sin ta tura mafi yawan sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa kasashen Afirka tsakanin zaunannun mambobi 5 na kwamitin sulhun MDD, ganin yadda take da sojojin 2500 da suke gudanar da aikinsu na kiyaye zaman lafiya a nahiyar Afirka. Ban da haka kuma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi alkawarin taimakawa tarayyar kasashen Afirka AU wajen kafa wata rundunar kiyaye zaman lafiya ta kanta, gami da tallafawa kokarin AU wajen kafa wata rundunar musammun da za ta iya mayar da martani cikin sauri game da abubuwan gaggawa dake faruwa ba zato ba tsammani. Dangane da wannan batu, a cewar He Wenping, yadda kasar Sin take taimakawa kasashen Afirka wajen tabbatar da tsaro yana da ma'ana sosai.

'Hakan zai sa kasashen Afirka samun karin tallafi a wannan fanni. Ya dade bayan da aka ba da shawarar kafa rudunar musamman ta AU, amma an kasa cimma wannan buri sakamakon karancin kudi da kayayyakin aiki. Yanzu tun da kasar Sin ita ma ta shiga cikin masu tallafawa kasashen Afirka a wannan fanni, to, zai sa su samu isasshen tallafi don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a nahiyar. Haka zalika, lamarin zai amfanawa kasar Sin, domin samun wani muhallin tsaro mai kyau a nahiyar Afirka shi ma zai ba da tabbaci ga ayyukanmu na hadin gwiwa a fannin tattalin arziki.'

Ban da haka kuma, wani abun da ya dace mu lura da shi shi ne, kasar Sin tana tsayawa kan manufarta ta tallafawa kasashen Afirka, domin ba kasashen Afirka damar jagorantar dukkan ayyukan da ake kokarin ba da tallafi kansu.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China