Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwararsa ta kasar Kenya madam Amina Mohamed sun gana da manema labaru bayan da suka yi shawarwari a tsakaninsu a birnin Nairobi, hedkwatar Kenya a ranar 10 ga wata.
Dangane da batun zuba jari kan shimfida hanyar dogo tsakanin Mombasa da Nairobi da kuma taimakawa shimfida hanyoyin dogo masu saurin tafiya a nahiyar Afirka, mista Wang ya ce, kasar Sin na son biyan bukatar Kenya ta raya ayyukan more zaman rayuwar jama'a. Haka kuma shimfida hanyar dogo a tsakanin Mombasa da Nairobi, mataki ne na farko wajen aiwatar da ra'ayi daya tsakanin shugabannin Sin da na Afirka kan shimfida hanyoyin dogo masu saurin tafiya a duk fadin nahiyar. Kasar Sin na son yin kokari wajen taimakawa kasashen Afirka cimma burinsu na shimfida hanyoyin dogo masu saurin tafiya a tsakaninsu. Mista Wang ya ce, ya yi imani da cewa, Sin da Afirka za su yi kokari tare wajen farfado da nahiyar Afirka ta hanyoyin dogo masu saurin tafiya, a karshe dai mutanen Afirka za su cimma burinsu. (Tasallah)