A yau ne Hong Lei, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya yi karin bayani kan yadda a ranar 12 ga wata, 'yan kasar Liberia 3 na farko suka murmure aka kuma sallame su daga cibiyar shawo kan cutar Ebola da kasar Sin ta taimakawa Liberia wajen gina ta. Lamarin ya nuna cewa, kasar Sin ta samu sakamako mai kyau wajen taimakawa Liberia a fannin yaki da cutar ta Ebola.
Mista Hong ya kara da cewa, samun nasarar warkar da masu fama da cutar Ebola a Liberia ya faranta ran kasar Sin kwarai da gaske. Kasar Sin tana son ci gaba da yin haka da kasashen duniya wajen kara taimakawa kasashen Afirka da cutar ta shafa da kuma jama'ar Afirka a fannin yaki da cutar ta Ebola mai kisa. (Tasallah)